Home Labarai Gwamnatin Kano ta magantu kan rikicin Rimin Zakara

Gwamnatin Kano ta magantu kan rikicin Rimin Zakara


Gwamnatin jihar Kano, ta ce za ta gudanar da bincike na musamman dangane musabbabin rikicin da ya faru a unguwar Rimin zakara, wanda yayi sanadiyyar rasa rayukan mutane uku da jikkata wasu da dama.

Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ne ya bayyana hakan a zantawarsa da manema labarai kan rikicin da aka samu tsakanin jami’an tsaro da mutanan dake zaune a yankin.

Waiya ya kuma ce jami’ar Bayero ce ta nemi taimakon gwamnatin Kano dan a dawo mata da filayenta, wanda hakan yasa ta shiga tsakani kuma aka baiwa mutanan dake zaune a gurin wa’adin tashi kasancewar lokacin da aka basu ya riga ya ƙare.

Daga nan waiya yace ɓata gari ne suka shiga cikin lamarin domin tada zaune tsaye duk kuwa da jami’an tsaron da waɗancen mutanen suka gayyato gudun tada fitina.

Kwamishinan yaɗa labarai da ayyukan cikin gida Kwamared Waiya yace, lallai Gwamnatin Kano zata kafa kwamitin da zai gudanar da bincike kan wanda suka haddasa rikicin da yayi sanadiyyar rayukan mutane.

Idan za a iya tunawa a ranar litinin ne al’ummar unguwar Rimin zakara suka zargi ma’aikatar ƙasa ta Kano da rushe musu gidaje da hadin kan jami’ar Bayero, lamarin da ya jawo har jami’an tsaro suka kashe mutane 3 tare da jikka wasu 16 .

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Gwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanciGwamnatin Najeriya da gwamnonin APC sun bai wa ƴan kasuwar Singer tallafin biliyan 8Kwankwasiyya ta yi martani kan matakin majalisar Amurka na hukunta KwankwasoSojojin Najeriya sun daƙile hare-haren mayaƙan ISWAP a BornoFarfesa Abdullahi Pakistan ya bayyana dalilinsa na ajiye shugaban Hukumar NAHCONMajalisar Najeriya ta kafa kwamitin nazari kan gyaran dokar zaɓeRundunar sojin Najeriya ta tura dakaru na musamman zuwa Filato don daƙile ƴanbindigaMajalisar Dinkin Duniya da Turkiya sun yi Alla-wadai da harin da aka kai KwaraAmurka ka iya sake kai Hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci- TrumpAmurka ka iya sake kai hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci
X whatsapp