Home General NNPP ta dakatar da jiga-jiganta hudu a Kano

NNPP ta dakatar da jiga-jiganta hudu a Kano

Jam’iyyar NNPP reshen Kano ta dakatar da wasu manyan mambobin ta hudu da suka hada da Sanata Kawu Sumaila, Ali Madakin Gini, Sani Abdullahi Rogo, da Kabiru Alhassan Rurum, bisa zarginsu da yiwa jam’iyyar zagon kasa.

Shugaban jam’iyyar na jihar Kano Hashimu Suleiman Dungurawa ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Kano.

Dungurawa yqace an zabi wadannan ‘yan majalisar dokokin ne a karkashin jam’iyyar NNPP amma a kwanakin baya suna yin wasu abubuwa da suka saba da Manufofi da akidar jam’iyyar.
Ya ce an ba su tikitin takara a jam’iyyar gabanin zabukan da suka gabata, amma maimakon su nuna godiya, sai suke yin abubuwan da suka ci karo da muradun jam’iyyar.

Wani lamari na baya-bayan nan da ya janyo dakatarwar shi ne yadda aka gudanar da daurin auren diyar Sanata Kawu Sumaila da kuma bikin yaye ɗaliban jami’ar kawu Sumaila.

Dungurawa ya bayyana mamakinsa da cewa wadanda suka halarci taron galibinsu mutane ne da su ka yaki Kawu a baya, amma kuma ya gayyatosu harkarsa kuma ya ki gayyatar ‘yan jam’iyya NNPP.

Shugaban jam’iyyar ya bayyana cewa za a kafa kwamitin da zai binciki lamarin tare da sanar da al’umma sakamakon karshe da jam’iyyar za ta dauka.

Duk da dakatarwar, Dungurawa ya jaddada cewa har yanzu akwai sauran damar tattaunawa ga wadanda aka dakatar din, idan har suka nemi afuwa jam’iyyar za ta iya yafe musu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp