Home General Badakala- Gwamnan Kano ya dakatar da mukaddashin Shugaban Ma’aikatan Jihar

Badakala- Gwamnan Kano ya dakatar da mukaddashin Shugaban Ma’aikatan Jihar

Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya dakatar da mai rikon mukamin shugaban ma’aikata kuma babban sakatare na Establishment Salisu Mustapha, bisa zargin zarge-zargen da ake yi na yanke albashin ma’aikatan gwamnatin Kano.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a ranar Alhamis, ya tabbatar da cewa an kuma umurci Salisu Mustapha da ya ajiye mukaminsa na babban Sakatare na Establishment, a karkashin ofishin shugaban ma’aikata, don ba da damar gudanar da bincike ba tare da tangarda ba.

Domin tabbatar da ci gaba da gudanar da harkokin mulki, gwamnan ya amince da nadin Malam Umar Muhammad Jalo, Babban Sakatare na REPA, a matsayin sabon shugaban ma’aikata na riko, har sai an kammala binciken da ake yi.

Gwamna Yusuf ya sake jaddada matsayinsa na kin amincewa da almundahanar kudi, yana mai gargadin cewa duk wanda aka samu da laifi zai fuskanci mummunan hukunci.

Kwamitin binciken da Abdulkadir Abdussalam ke jagoranta da aka kaddamar a yau, an ba shi wa’adin kwanaki bakwai don gano inda matsalar ta ke tare da gabatar da sakamakon binciken.

A farkon wannan watan ne aka nada Salisu Mustapha a matsayin shugaban ma’aikata na riko, biyo bayan hutun jinya da aka baiwa babban shugaban ma’aikatan, Abdullahi Musa, wanda yanzu haka yake jinya a kasar Indiya.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Gwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanciGwamnatin Najeriya da gwamnonin APC sun bai wa ƴan kasuwar Singer tallafin biliyan 8Kwankwasiyya ta yi martani kan matakin majalisar Amurka na hukunta KwankwasoSojojin Najeriya sun daƙile hare-haren mayaƙan ISWAP a BornoFarfesa Abdullahi Pakistan ya bayyana dalilinsa na ajiye shugaban Hukumar NAHCONMajalisar Najeriya ta kafa kwamitin nazari kan gyaran dokar zaɓeRundunar sojin Najeriya ta tura dakaru na musamman zuwa Filato don daƙile ƴanbindigaMajalisar Dinkin Duniya da Turkiya sun yi Alla-wadai da harin da aka kai KwaraAmurka ka iya sake kai Hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci- TrumpAmurka ka iya sake kai hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci
X whatsapp