Majalisar Dattawa ta dakatar da Sanata Natasha na tsahon watannin 6

Majalisar dattawan Najeriyar dai ta ɗauki matakin dakatar da sanatar ne har na tsawon watanni shida bisa shawarwarin da kwamitin Ɗa’a da Ladabtarwa da Sauraron ƙorafin Jama’a na majalisar ya bayar, bayan nazari kan ƙorafin da sanata Natasha ta miƙa wa majalisar ranar Laraba.

Shugaban kwamatin, Sanata Neda Imasuen shi ne ya bayar da shawarwarin bayan karanto jerin laifuka da kwamitin ya ce ya samu Sanata Natasha da aikatawa a majalisar.

Da yake karanta bayanin dakatarwar, shugaban majalisar, Sanata Godswill Akpabio wanda a kansa ne Sanata Natasha ke ƙorafin cin zarafi na lalata, ya nemi jin ra’ayin ƴan majalisar kan su amince ko su ƙi amincewa da dakatarwar ta tsawon watanni shida amma kuma za a iya rage yawan lokacin idan har ta rubuto takardar neman afuwa. Ƴan majalisar kuma sun amince da hakan.

Da ma dai tunda farko sai da kwamitin na Ɗa’a da Ladabtarwa da Sauraron ƙorafin Jama’a na majalisar ya yi watsi da ƙorafin sanata Natasha bisa dalilan cewa ƙorafin da Sanata Natasha ta shigar ranar Laraba bai cika ƙa’ida ba saboda ita mai ƙorafin da kanta ta sanya hannu kan ƙorafin maimakon ta bai wa wani ya shigar da shi a madadinta, lamarin da ya ce ya lalata ƙorafin nata tun ba a je ko’ina ba.

Ya kuma ƙara da cewa batutuwan da ke cikin ƙorafin na gaban kotu a yanzu haka, wanda ya sa ba za a iya tattauna su ba kuma majalisar ba ta da hurumin sauraron su.

Kafin dai shugaban majalisar ta dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya sanar da dakatar da Sanata Natasha sai da aka bai wa ƴan majalisar dattawan da dama suka faɗi albarkacin bakinsu inda ba tare da ragin ɗaka ba suka goyi bayan hukuncin.

Sai dai shugaban marasa rinjaye na majalisar ta dattawa, Sanata Patrick Abba Moro na jam’iyyar PDP wanda shi ma ya ƙwanƙwashi Sanata Natasha amma ya nemi majalisar ta yi wa ƴar majalisar sassauci inda ya ce a rage tsawon lokacin dakatarwar daga watanni shida zuwa uku.

Sanata Natasha ta yi wuf ta ce “wannan rashin adalci ba zai ɗore ba”, kafin a kashe abin maganarta.

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1463 days 2 hours 19 minutes 49 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1445 days 4 hours 1 minute 14 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com