Za a yi wa ɗalibai riga-kafin Diphtheria a Legas bayan mutuwar wani ɗalibi

Jam’ian kiwon lafiya a jihar Legas sun ƙaddamar da shirin riga-kafi na gaggawa bayan samun ɓarkewar cutar Diphtheria da ya yi sanadiyyar mutuwar wani ɗalibi mai shekara 12 a wata makarantar sakandare.

Aƙalla mutane 34 suka yi mu’amala da shi kuma ana sanya musu ido, yayin da ɗalibai 14 daga makarantar kwanan mai suna King’s College suka nuna alamu kuma aka tabbatar da cewa 12 daga cikinsu na da cutar, inda tuni aka fara ba su magani.

A cewar ma’aikatar lafiya ta jihar Legas, yaron ya fara nuna alamu ne na ciwon maƙoshi da kuma zazzaɓi a cibiyar lafiya ta makarantar a ranar 22 ga watan Fabrairu, inda kuma ya rasu a ranar 6 ga watan Maris.

A yanzu haka an fara gangamin yi wa mutane riga-kafi musamman yara da jam’ian kula da lafiya na makarantar, wanda hukumomi ke ganin za a faɗaɗa shi zuwa jihar baki-ɗaya.

Wata takardar gargaɗi kan lafiya ta buƙaci mazauna jihar su mayar da hankali kan tsafta da kuma guje wa shiga cunkoson mutane kuma su garzaya asibiti da zarar sun fara jin alamu irin na cutar diphtheria.

Kwamishinan lafiya na jihar Farfesa Akin Abayomi ya tabbatar wa da alumma cewa babu buƙatar su tayar da hankalinsu ganin cewa ana iya ƙoƙari wajen daƙile ɓarkewar cutar, kuma za a ci gaba da ɗaukar matakai domin kare su daga kamuwa da ita.

A shekarar 2023 ne aka samu ɓarkewar cutar diphtheria mafi girma a Najeriya inda ta yi sanadiyyar mutuwar mutane fiye da 600 akasari yara, kuma cutar ta shafi jihohi 19 cikin 36 da ke ƙasar.

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1462 days 20 hours 14 minutes 51 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1444 days 21 hours 56 minutes 16 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com