Home General Na fuskanci tarin kalubale a lokacin da na karbi mulki-Tinubu

Na fuskanci tarin kalubale a lokacin da na karbi mulki-Tinubu

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya ce sauye-sauyen tattalin arziki da gwamnatinsa ke yi, tana yi ne da nufin gyara makomar yara masu tasowa.

Yayin da yake jawabi ga ƙungiyar ƴan majalisa ta uku – wadda ya kasance cikin a Jamhuriya ta uku – da suka kai masa ziyara a fadarsa, Shugaba Tinubu ya ce a baya ƙasar na kashe kuɗaɗen yaran ƙasar da ba a kai ga haihuwarsa ba.

“Shekara 50 da suka gabata, Najeriya na kashe kuɗaɗen yaran da ba a kai ga haihuwarsu ba, tare da mayar da hankali kan man fetur wajen samun kuɗin shiga. Ba a yi wani tsari na tallafa wa yaran da za a haifa a gaba ba,” kamar yadda ya ce.

Shugaban ya kuma bayyana tarin matsalolin da ya fuskanta a farkon mulkinsa, musamman fannin tattalin arzikin da rayuwar jama’a.

“Mun fuskanci tarin ƙalubale a lokacin da na karɓi mulki. Inda ba mu ɗauki matakai ba da yanzu ƙasar ta talauce, kuma ai haƙƙinmu ne mu kare tattalin arzikinmu daga rugujewa”, in ji Shugaba Tinubu.

To amma shugaban ya ce a yanzu kwalliya ta fara biyan kuɗin sabulu dangane da sauye-sauyen da gwamatinsa ta fara ɓullo da su.

“Amma a yau bayan shimfiɗa mai kyau da muka yi, mun smau nasarar magance matsalolin da suka tunkaro ƙasarmu, a yanzu canjin kuɗi ya daidaita, farashin abinci na ci gaba da sauka, musamman a lokacin Ramadan, da yardar Allah wahalar ta zo ƙarshe”, a cewar shugaban na Najeriya.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp