Kuɗin shiga na MTN ya ƙaru da kashi 35.6 a watan Maris bayan ƙarin kuɗin kira da data da kamfanin ya yi a watan Fabrairu.
A wani rahoto da ofishin kamfanin na Afirka ta Kudu ya fitar a ranar Litinin, ya ce suna sa ran kuɗin da shigansu zai cigaba da ƙaruwa a wannan shekarar ta 2025.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin kamfanin ya samu karyewar arziki a jimillar kuɗin shiga na shekara da kaso 69 saboda karyewar darajar naira da matsalolin da suka fuskanta a Sudan a sanadiyar yaƙi, kamar yadda tashar Channels ta ruwaito.
Sai dai duk da matsalolin karyewar darajar naira da yaƙin na Sudan, babban jami’in gudanarwa na kamfanin, Ralph Mupita ya ce suna ganin alamar haske a gaba
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1486 days 22 hours 37 minutes 4 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1469 days 18 minutes 29 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021
Report By: PRNigeria.com