Jami’an tsaro a jihar Katsina sun samu nasarar daƙile yunƙurin ƴanbindiga na kai hari a ƙaramar hukumar Ɗanmusa da ke jiyar, wadda take arewa maso yammacin ƙasar.
Kakakin rundunar ƴansandan jihar Katsina, DSP Abubakar Sadiq ya bayyana a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, inda ya ce jami’an tsaron sun samu nasarar ne a ranar Asabar.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
“A ranar 15 ga watan Maris ce jami’an tsaron farin kaya suka samu bayanan sirri cewa ƴanbindiga suna taruwa a tsaunin Maijele da ke ƙaramar hukumar Ɗanmusa domin kai hari a ƙauyen Ɗan Takuri.
“Da samun labarin ne jami’an tsaron haɗin gwiwa na ƴansanda da askawaran Katsina suka kai ɗauki, inda aka yi musayar wuta tsakanin ƴanbindigar da jami’an tsaro.”
Ya ce a ƙarshe dai jami’an tsaron sun samu nasarar fatattakar ƴanbindigar, tare da kashe ɗaya daga cikinsu, sannan aka ƙwato wasu makamai da ƙwayoyi.











