Home General Dakatar da gwamnan Rivers bata sunan Najeriya ne a idon duniya –...

Dakatar da gwamnan Rivers bata sunan Najeriya ne a idon duniya – Jonathan

Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya soki dakatar da gwamnan jihar Rivers da mataimakiyarsa da ƴanmajalisar dokokin jihar, wanda shugaban ƙasar, Bola Tinubu ya yi.

Jonathan ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a matsayin shugaban taro wanda gidauniyar Haske Satumari ta shirya a ranar Asabar a Abuja, inda ya bayyana rashin jin daɗinsa kan matakin na cire zaɓaɓɓun shugabanni.

“Wannan matakin da aka ɗauki zai ɓata sunan Najeriya ne a idon duniya,” in ji shi, kamar yadda tashar Channels ta ruwaito.

Jonathan ya ce duk da cewar akwai buƙatar ɗaukar matakan da za su magance rikicin siyasar da ya dabaibaye jihar Rivers na tsawon lokaci, a cewarsa dakatar da waɗanda mutane suka zaɓa a matsayin shugabanninsu bai dace ba.

Ya ƙara da cewa ya san bai kamata a matsayinsa tsohon shugaban ƙasa ya cika maganganu barkatai a game da abubuwan da suke a ƙasar ba, amma “yadda ake kallon Najeriya yana ta’allaƙa ne a kan matakan ɓangaren zartaswa da majalisa da na shari’a suka ɗauka,” in ji shi.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp