Home General ‘Yanbindiga sun kashe jami’an tsaro 10 a jihar Zamfara

‘Yanbindiga sun kashe jami’an tsaro 10 a jihar Zamfara

‘Yanfashin daji sun kashe dakarun rundunar tsaro a jihar Zamfara 10 a wani kwanton ɓauna da suka yi musu ranar Asabar.

Gwamnan Zamfara Dauda Lawal ya ce shida daga ciki dakarun tsaron gwamnatin jihar ne da ake kira Askarawa, huɗu kuma ‘yan sa-kai ne.

Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, gwamnan ya ƙara da cewa akwai dakarun Asakarawa biyu da ɗan sa-kai ɗaya da suka ɓata.

“Lamarin ya faru ne bayan farmakin da gamayyar jami’an tsaro [ciki har da Askarawa] ƙarƙashin jagorancin sojojin Najeriya suka kai wa sansanin ‘yanbindiga a Dajin Sunƙe, wanda aka samu gagarumar nasarar kashe da dama tare da ƙwato makamai masu tarin yawa,” in ji Gwamna Lawal.

Ya ce tuni aka yi jana’izarsu a yau Lahadi, yana mai cewa ya bayar da umarnin ɗaukar “matakin bayar da agajin gaggawa ga waɗanda suka ji raunuka” da kuma “bayar da tallafin gaggawa ga iyalan waɗanda suka rasu”.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp