Majalisar ƙoli ta harkokin addinin musulunci a Najeriya ƙarƙashin jagorancin mai alfarma Sarkin Musulmi Alh. Muhammad Sa’ad Abubakar ya bayyana cewa akwai yuwar a ci gaba da azumi a ranar Lahadi domin zuwa yanzu ba’a ga wata a Najeriya ba.
Majalisar ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da babban sakatareta Farfesa Ishaq Oloyede ya sanya wa hannu a yau Asabar.
Read Also:
“Idan Musulmai suka ga jinjirin wata bisa ga ka’idojin ganin watan, to mai alfarma zai bayyana ranar Lahadi 30 ga Maris, 2025 a matsayin 1 ga Shawwal da kuma ranar Idul Fitr.”
Idan daibzaku iya tunawa da yammacin wannan Rana hukumomi a kasar Saudiyya suka tabbatar da ganin jinjirin watar na karamar sallah Wanda ke bayyana ranar lahadi zasu gabatar da salla.