Home General Dole a kawo ƙarshen kisan gilla da ake yi wa ƴan arewa...

Dole a kawo ƙarshen kisan gilla da ake yi wa ƴan arewa a kudancin Najeriya – Dattawan Arewa

Ƙungiyar dattawan arewa ta magantu kan kisan matafiya ƴan yankin arewa da aka yi a garin Uromi da ke jihar Edo, inda ta ce yankin arewa ya daɗe yana haƙuri da cin kashin da ake yi masa, amma kuma an kusa ƙure su.

Ƙungiyar ta bayyana haka ne a wata sanarwa da kakakinta, Farfesa Abubakar Jika Jiddere ya fitar, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Sanarwar ta ce, “dattawan arewa sun damu matuƙa da kisan dabbanci da rashin tausayi da aka yi wasu mafarauta ƴan arewa da suke hanyarsu ta komawa gida arewa domin bikin sallah. Muna Allah wadai da wannan aika-aikar.

“Mun daɗe muna haƙuri da irin wannan cin kashin da ake mana a kudancin Najeriya. Dole a kawo ƙarshensa haka,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa dole a kama waɗanda suka aikata laifin, sannan a musu hukunci a bayyane.

“Sannan dole a biya diyyar waɗanda aka kashe kamar yadda yake a addinance, sannan dole gwamnatin Edo ta fito ta bayar da haƙuri.

Dattawan sun kuma buƙaci gwamnatin tarayya da ta Edo ta cika waɗannan buƙatun nan da kwana da 14, “idan kuma ba a ga wani mataki ba zuwa lokacin, dattawan arewa za su yi amfani da duk matakan da suka dace wajen bin haƙƙin ƴaƴanta da aka kashe.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp