Masarautar Kano ta yi rashin guda daga cikin manyan jagorin da su ka yi shura wurin al,amuran mulki da jagoranci shekaru masu tsawo, Galadiman Kano Alhaji Abbas Sanusi, dan sarkin Kano Abbas Abdullahi Bayero.
Galadiman Kano, Alhaji Abbas Sanusi ya rasu ya na da shekaru 92 a duniya, a ranar talata da dare.
Ya kasance jigogin cikin wadanda da suka shahara a Masarautar Kano. A zamanin marigayi Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero, shi ne Wamban Kano, Kuma Babban Dan majalisar Sarki.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Shugaban Jam’iyyar APC a jihar Kano, Alhaji Abdullahi Abbas da Dan uwansa, Alhaji Kabiru Abbas su ne su ka tabbatar da rasuwar mahaifin na su bayan jinya da ya yi ta tsawon lokaci.
Rasuwar marigayi Galadiman Kano rashi ne ga al’ummar Arewacin Nijeriya ba ma iya masarautar kano ba kadai.
Ya rike mukamai daban-daban, karkashin Sarkin Kano Ado Bayero, wanda ya kasance a karagar masarautar daga shekarar 1963 zuwa 2014.
Ya rasu ya bar mata da ‘yaya 35, daga cikinsu akwai shugaban jami’iyyar APC na jihar Kano, Alhaji Abdullahi Abbas.
Za a gudanar da jana’izarsa a fadar masarautar Kano, dake kofar kudu da karfe 9 na safiyar ranar larabar nan.











