Rahotannin daga jihar Borno da ke arewa maso gabashin Nijeriya na bayyana cewa wasu da ake zargin mayakan Boko Haram ne sun kai hari sansanin horas da ‘yan sanda na PMFTC da ke Limankara, a Gwoza, inda suka kashe Sufeton ’yan sanda guda ɗaya.
Sun kai harin da misalin ƙarfe 6 na safiyar ranar Alhamis, 3 ga watan Afrilu, 2025, yayin da jami’an tsaro suka fita sintiri a ƙafa.
Read Also:
Sufeto Andrawus Musa daga rundunar 6PMF da ke Maiduguri ya samu rauni a harin, inda maharan suka ƙwace bindigarsa ƙirar AK-47.
An kai shi asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri (UMTH), amma rai ya yi halinsa.
Rundunar dai na gudanar da bincike kan harin, tare da ƙoƙarin ganin ta kama waɗanda suka kai hari.
Ta kuma nemi jama’a da suke sanya ido kan duk wani abun zargi, tare da bai wa jami’an tsaro rahoto.