Rahotanni daga Najeriya, na bayyana cewa wasu kamfanonin sufurin hajji da umarah na kasar sun bayyana janyewarsu daga hada-hadar aikin hajjin bana, saboda yadda suka ce hukumar alhazan Najeriyar tana gudanar da wasu ayyuka da kamfanonin ya kamata su riƙa aiwatarwa.
Malam Haruna Isma’il shugaban ɗaya daga cikin kamfanonin uku, ya ce sun kwashe tsawon shekara uku suna neman a yi gyara, amma ba a yi komai ba.
Read Also:
Malam Haruna Isma’il shugaban kamfanin harkar sufurin hajji da umarah na Annur Air Services ya karan-tsaye da wuce gona da iri da acewarsa suke cutar da alhazai da masu harkar jigilar ne suka sa suka yanke shawarar janyewa daga aikin.
Mun dai nemi jin ta bakin jami’ar hulɗa da jama’a ta hukumar alhazai ta Najeriya, wadda ta yi alƙawarin aiko mana da nasu martanin kan wannan batu, amma har ya zuwa yanzu babu bayani daga wajenta ba.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1485 days 14 hours 39 minutes 46 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1467 days 16 hours 21 minutes 11 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com