Ƙasashen AES sun yi wa jakadunsu a Aljeriya ƙiranye

Ƙasashen kungiyar  AES sun yi wa jakadunsu da ke Aljeriya kiranye a jiya lahadi ,bayan Mali ta zargi kasar da ƙaƙƙabo wani jirgin yakinta mara matuki a kusa da Tinzaouatene.

A cikin  daren 31 ga watan Maris da ya gabata wayewa safiyar 1 ga watan nan na Afrilu Aljeriya ta sanar da ƙaƙƙabo wani jirgi mara matuki mallakin sojojin Mali da ta zarga da keta sararin samaniyarta a kusa da Tinzaouatene da ke kan iyakar kasashen biyu.

A wata sanarwa da suka fitar a jiya lahadi kasashen AES wato Mali,Nijar da Burkina Faso sun bayyana bakin cikinsu da afkuwa lamarin tareda jaddada cewa kai hari kan daya daga cikin kasashen tamkar kaiwa baki dayan kungiyar hari ne.

Ministan harakokin wajen Mali Abdoulaye Diop ya bayyana lamarin da mai matukar muni ,lura da yadda tarwatsa jirgin ya hana dakarun kasar  cimma burinsu na ƙaƙƙabe wani gungun ‘yan ta’adda da ke tsara kai hare-hare kan kasashen AES.

Ƙasashen na  AES wato Mali da Nijar da kuma Burkina Faso sun zargi Aljeriya da taƙalar fada sanan sun sha alwashin kai kararta a gaban hukumomin ƙasa da ƙasa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com