Hedkwatar tsaron Najeriya ta ce babu kuɗin fansa da aka biya kafin sakin tsohon shugaban Hukumar yi wa Ƙasa Hidima a Najeriya NYSC, Manjo Janar Mahrazu Tsiga, mai ritaya daga hannun ƴanbindiga.
Wata sanarwa da mai magana da yawun hedkwatar tsaron Birgediya-Janar Tukur Gusau ya fitar, ya ce sojoji sun yi amfani da dabarun karfi da kuma bayanan sirri wajen ceto Janar Tsiga.
“Tun bayan sace Janar Tsiga ranar 7 ga watan Fabrairu, sojoji ba su yi ƙasa a gwiwa ba. Sun kai samame ta sama da kuma ƙasa a ƙananan hukumomin Ɗanmusa da Faskari da kuma Kankara inda ake kyautata zaton masu garkuwan sun ajiye shi,” a cewar Tukur Gusau.
Sanarwar ta ƙara da cewa sojojin sun yi ta aiki tukuru babu dare ba rana wajen nema da kuma ceto tsohon shugaban na NYSC.
An dai yi garkuwa da shi ne ranar 5 ga watan Fabrairu, a garin mahaifarsa ta Tsiga da ke karamar hukumar Bakori na jihar Katsina – tare da wasu mutum 13.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1485 days 14 hours 39 minutes 40 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1467 days 16 hours 21 minutes 5 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com