Kwamitin yaƙi da dabanci a Kano ya ce ya samu nasarar kama ɓatagari sama da 400

A jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya, kwamitin kar-ta-kwana kan yaƙi da ayyukan daba da dawo da zaman lafiya da gyaran halin matasa, ya sanar da kama ɓata-gari fiye da 400.

Kwamitin ya ce daga cikin waɗanda aka kama ɗin, an yankewa kashi 70 cikin 100 a cikinsu hukunci.

Matsalar daba da ƙwacen waya dai, sun sa jama’a a Kano na rayuwa cikin firgici tare da ƙauracewa fitar dare da kuma yin taka tsan-tsan da rana kasancewar harin daba na iya rutsawa da mutum a kowane lokaci.

Dr Yusuf Ibrahim Kofarmata shi ne shugaban kwamitin kuma ya ce zuwa yanzu sun samu nasarorin da aka daɗe ba a samu ba.

Ya ce, “aiki ne babba, amma suna aiki sosai domin shiga lungu da saƙo tare da taimakon jami’an tsaro. Kuma muna da kotun ta fi da gidanka, inda muke yanke hukunci nan take

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1486 days 1 hour 2 minutes 38 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1468 days 2 hours 44 minutes 3 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com