Home General Ganduje ya caccaki hadakar su Atiku Abubakar

Ganduje ya caccaki hadakar su Atiku Abubakar

Shugaban Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya, Abdullahi Umar Ganduje ya ce duk wata haɗaka da jam’iyyun hamayyar ƙasar ke shirin yi da nufin kawar da APC a zaɓen 2027 ba za ta yi tasiri ba.

Ganduje ya bayyana hakan ne lokacin da yake jawabi ga manema labarai a jihar Kaduna lokacin ziyarar da ya jagoranci shugabannin jam’iyyar wajen kai wa tsohon shugaban ƙasar – Muhammadu Buhari.

Gabanin ziyarar su Gandujen, tawagar jagoran adawar ƙasar, Atiku Abubakar tare da tsoffin gwamnonin jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai da Sanata Ahmed Makarfi da kuma Sanata Aminu Waziri Tambuwal ta fara kai wa Buhari ziyara a gidan nasa.

Ganduje ya ce ziyarar su Atikun ba ta ɗaga musu hankali ba, saboda a cewarsa ”suna son ƙulla wata haɗaka da ba za ta yi tasiri ba”.

”Daga abin da muka gani mutane ne da ba za su iya haɗuwa ƙarƙashin inuwa guda ba”, in ji shi.

Shugaban jam’iyyar ta APC ya ce a shirye suke kuma sun san yadda za su ɓullo wa lamarin kodayake ya ce ba zai faɗi dabarar da za su bi ba.

Ganduke ya ce duk da cewa a yanzu haka APC na da iko da jihohin ƙasar 21, har yanzu jam’iyyarsu na hangen ƙarin wasu jihohin.

”Ko dai wasu gwamnonin da kansu su dawo jam’iyyarmu, ko kuma jihohin su dawo hannunmu ta hanyar zaɓe.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp