Home General Sojojin Najeriya sun hallaka ƙasurgumin ɗanbindiga Gwaska da wasu guda 100

Sojojin Najeriya sun hallaka ƙasurgumin ɗanbindiga Gwaska da wasu guda 100

Hukumomi a Najeriya sun ce jami’an tsaron ƙasar sun halaka ƴanbindiga 100 ciki har da gawurtaccen ɗanbindiga, Gwaska a jihar Katsina da ke Arewa Maso Yammacin Ƙasar.

Hadin gwiwar jami’an tsaron kasar ne suka ƙaddamar da harin a ranar Juma’a wanda ya yi sanadin kisan Gwaska – wanda ya kasance mataimakin shahararren ɗanbindiga Malan, shugaban ISWAP a yankin Arewa Maso Yamma.

Bayanai sun nuna cewa Gwaska Dankarami ya jima yana ɓuya a dajin Munumu da ke jihar Katsina.

Rahotonni sun ce sojojin sun lalata maɓoyar ƴanbindigar da dama a sassan jihar a lokacin harin, tare da ƙwato da kuma lalata wasu manyan bindigogi masu jigida da waɗanda aka ƙera a cikin gida.

Harin na zuwa ne bayan da a farkon mako ƴanbindigar suka yi garkuwa da mutum 43 mazauna ƙauyukan Maigora da ke yankin ƙaramar hukumar Dandume

Kwamishinan al’amuran cikin gida na jihar Katsina, Nasir Mu’azu ya bayyana matakin da wata gagarumar nasara a yaƙi da ƴanbindiga ake yi a jihar.

“Abin farin ciki ne ga jihar, domin wannan nasara ta taimaka wajen wargaza hadakar ƴanbindigar da ke addamar garuruwa da ƙauyukan yankunan ƙananan hukumomin Faskari da Kankara da Bakori da Malumfashi da kuma Kafur,” in ji Kwamishinan.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp