Home General Natasha ta bukaci a dawo mata da Jami’an tsaron da ak janye...

Natasha ta bukaci a dawo mata da Jami’an tsaron da ak janye mata

Ƴar Majalisar Dattawan Najeriya, mai wakilitar Kogi ta Tsakiya, Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan – da aka dakatar – ta yi kira ga babban sifeton ƴansandan ƙasar, ya mayar mata da jami’an tsaronta da aka janye mata lokacin da majalisa ta dakatar da ita.

Kiran na zuwa ne bayan da wasu mahara suka auka wa gidan kakanninta da ke jihar Kogi ranar Talatar da ta gabata.

Jaridun Najeriya sun ambato wata sanarwa da ofishin yaɗa labaran ƴar majalisar ya fitar, na cewa an kai harin ne a lokacin da ƙaninta ya je garin domin duba wani aikin mazaɓu da Natasha ke gudanarwa a garinta na Obeiba-Ihima.

Sanata Natasha ta yi zargin cewa ita aka ƙudiri aniyar kai wa harin, tana mai cewa maharan sun kai harin ne saboda a tunaninsu tana gidan.

Harin ya lalata wasu ɓangarorin gidan, wanda ƴar majalisar ta ce na kakanta ne.

To sai dai jami’an tsaro sun yi asarar daƙile harin, kamar yadda ta yi ƙarin haske.

A watan da ya gabata ne dai Majalisar Dattawan Najeriyar ta dakatar da ƴar majalisar tsawo wata shida, tare da tsayar da alawus-alawus da ake ba ta da jami’an tsaron da ke ba ta kariya, saboda zargin rashin ɗa’a.

Dakatarwar na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan ta zargi Shugaban Majalisar Dattawan Ƙasar, Sanata Godswill Akpabio da yunƙurin cin zarafi na lalata da amfani da ofishinsa wajen tursasawa da kuma daƙile mata aikinta.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Gwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanciGwamnatin Najeriya da gwamnonin APC sun bai wa ƴan kasuwar Singer tallafin biliyan 8Kwankwasiyya ta yi martani kan matakin majalisar Amurka na hukunta KwankwasoSojojin Najeriya sun daƙile hare-haren mayaƙan ISWAP a BornoFarfesa Abdullahi Pakistan ya bayyana dalilinsa na ajiye shugaban Hukumar NAHCONMajalisar Najeriya ta kafa kwamitin nazari kan gyaran dokar zaɓeRundunar sojin Najeriya ta tura dakaru na musamman zuwa Filato don daƙile ƴanbindigaMajalisar Dinkin Duniya da Turkiya sun yi Alla-wadai da harin da aka kai KwaraAmurka ka iya sake kai Hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci- TrumpAmurka ka iya sake kai hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci
X whatsapp