Home General hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano ta fara raba kayan aikin...

hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano ta fara raba kayan aikin hajjin bana

Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano dake Arewa maso yammacin Nijeriya ta fara raba kayan aikin hajjin bana ga maniyyata.

Wannan na kunshe ta cikin wata sanarwa da Jami’in Yada Labarai da Hulda da Jama’a na hukumar Sulaiman A. Dederi ya fita kuma aka raba manema labarai a jihar.

sanarwar ta ce Darakta Janar na Hukumar , Alhaji Lamin Rabi’u Danbappa, ya fara rabon muhimman kayayyakin aikin Hajji ga alhazan jihar da za su tafi kasa mai tsarki.

Alhaji Lamin Rabi’u ya bukaci dukkan masu shirin zuwa aikin Hajji da su yi amfani da kayan da aka raba yadda ya kamata, tare da kaucewa daukar wasu kayayya da hukumar kasar Saudi Arabia ta haramta

Haka kuma, ya umurci dukkan alhazai da su tuntuɓi jami’an aikin Hajji na kananan hukumominsu domin karɓar kayayyakin.

Bugu da ƙari, Alhaji Lamin Rabi’u Danbappa ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta Najeriya, ta hannun Hukumar Hajji ta Kasa (NAHCON), da ta sake duba batun amfani da katin ATM wajen bayar da kudin alhazai. Ya jaddada bukatar bayar da kuɗaɗen tafiya (BTA) a matsayin kuɗi na hannu domin sauƙaƙa wa alhazai samun damar amfani da su.

A nasa bangaren, Shugaban Majalisar, Daraktoci na hukumar Alhaji Yusif Lawan, ya shawarci alhazan da su yi amfani da kayan da aka raba yadda ya dace.

Kayayyakin da ake rabawa sun haɗa da: jakunkunan hannu, kayan suttura na maza da na mata, hijabai, zobunan hannu , da kananan jakunkuna domin ajiye kuɗi da muhimman takardu.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Gwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanciGwamnatin Najeriya da gwamnonin APC sun bai wa ƴan kasuwar Singer tallafin biliyan 8Kwankwasiyya ta yi martani kan matakin majalisar Amurka na hukunta KwankwasoSojojin Najeriya sun daƙile hare-haren mayaƙan ISWAP a BornoFarfesa Abdullahi Pakistan ya bayyana dalilinsa na ajiye shugaban Hukumar NAHCONMajalisar Najeriya ta kafa kwamitin nazari kan gyaran dokar zaɓeRundunar sojin Najeriya ta tura dakaru na musamman zuwa Filato don daƙile ƴanbindigaMajalisar Dinkin Duniya da Turkiya sun yi Alla-wadai da harin da aka kai KwaraAmurka ka iya sake kai Hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci- TrumpAmurka ka iya sake kai hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci
X whatsapp