Home General Aranposu ya bayar da tallafin magunguna ga hukumar KAROTA

Aranposu ya bayar da tallafin magunguna ga hukumar KAROTA

Mataimakain shugaban hukumar da ke lura da zirga-zirgar ababan hawa ta jihar Kano, KAROTA, Alhaji. Auwal Shuáibu Aranposu, ya bayar da tallafin maganguna ga asibitin hukumar domin inganta walwala da jin dadin ma’aikata.

Aranposu ya bayyana hakan ne yayin da yake ganawa da manema labarai, in da ya ce hakan na matsayin wani mataki na lura gami da inganta lafiyar jami’an hukumar, wadanda mafi yawan ayyukansu suna yi ne akan titinan jihar wajen dake da hadari.

Ya kuma kara da jan hankalin jami’an hukumar wajen kara lura a lokacin da suke tsaka da gudanar da aiki, sannan ya bukaci su da su yi amfani da asibitin yadda ya kamata.

Haka kuma ya bukaci malaman lafiyar da ke asibiti su yi amfani da magungunan yadda ya dace domin amfanin ma’aikatan hukumar.

Haka kuma ya kara tabbatarwa da jami’an irin yunkurin da hukumar ke yi waje ganin ta kare lafiya da rayukan dakarunta a dukkan in da suka sami kan su.

Daga bisani Aranposu ya yaba da kokarin jami’an wajen jajircewarsu a yayin da suke gudanar da ayyukansu, in da ya bukaci da su dore da hakan domin cigaban hukumar da jihar Kano.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Gwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanciGwamnatin Najeriya da gwamnonin APC sun bai wa ƴan kasuwar Singer tallafin biliyan 8Kwankwasiyya ta yi martani kan matakin majalisar Amurka na hukunta KwankwasoSojojin Najeriya sun daƙile hare-haren mayaƙan ISWAP a BornoFarfesa Abdullahi Pakistan ya bayyana dalilinsa na ajiye shugaban Hukumar NAHCONMajalisar Najeriya ta kafa kwamitin nazari kan gyaran dokar zaɓeRundunar sojin Najeriya ta tura dakaru na musamman zuwa Filato don daƙile ƴanbindigaMajalisar Dinkin Duniya da Turkiya sun yi Alla-wadai da harin da aka kai KwaraAmurka ka iya sake kai Hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci- TrumpAmurka ka iya sake kai hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci
X whatsapp