Home General Adadin kuɗin shigar Dangote zai kai dala biliyan 30 a shekara mai...

Adadin kuɗin shigar Dangote zai kai dala biliyan 30 a shekara mai zuwa

Fitaccen attajirin Nahiyar Afirka Aliko Dangote ya ce zai samu kuɗin shiga a dukkanin hada-hadar kasuwancisa da ta kai dala biliyan 30 a shekara mai zuwa, dukda yadda harajin Amurka zai shafi kamfanoninshi.

Shugaban rukunin kamfanonin na Dangote ya ce kasuwancinsa da suka haɗa da matatar man fetur mai ƙarfin tace ganga dubu 650 a kullum zai ƙaru da dala biliyan 5 a shekarar 2026.

Adadin kuɗin shigar kamfanonin na Dangote dai a wannan shekarar ya kai dala biliyan 25 abin da ke nufin idan an samu ƙarin dala biliyan 5 zai kama dala biliyan 30 a baɗi.

Shugaban Amurka Donlad Trump ya ware fannin mai da gas daga ƙarin haraji abin da ya sa matatar Dangote ci gaba da shigar da mai  a ƙasar. Baya ga haka Dangote na kai taki ƙasar ta Amurka.

Adadin harajin shigar da kaya da Najeriya ke biyan Amurka ya yi ƙasa da kashi 16 idan aka kwatanta da wanda Algeria ke biyan ƙasar, abin da ya bai wa ƙasar damar hada-hadar kasuwanci fiye da Algeria.

Dangote ya ce ya damu da harajin da Amurka ta sanya, saboda kashi 37 na takin da yake sayarwa na Urea yana zuwa Amurka ne. sai dai sun yi sa a ita ƙasar Algeria an ƙaƙaba mata kashi 30 na haraji.

A gefe guda kuma ana hasashen Dangote zai zama babban mai fitar da siminti a nahiyar Afirka a shekara mai zuwa, inda zai iya kere ƙasar Masar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Gwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanciGwamnatin Najeriya da gwamnonin APC sun bai wa ƴan kasuwar Singer tallafin biliyan 8Kwankwasiyya ta yi martani kan matakin majalisar Amurka na hukunta KwankwasoSojojin Najeriya sun daƙile hare-haren mayaƙan ISWAP a BornoFarfesa Abdullahi Pakistan ya bayyana dalilinsa na ajiye shugaban Hukumar NAHCONMajalisar Najeriya ta kafa kwamitin nazari kan gyaran dokar zaɓeRundunar sojin Najeriya ta tura dakaru na musamman zuwa Filato don daƙile ƴanbindigaMajalisar Dinkin Duniya da Turkiya sun yi Alla-wadai da harin da aka kai KwaraAmurka ka iya sake kai Hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci- TrumpAmurka ka iya sake kai hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci
X whatsapp