Shugaban Najeriya Bola Tinubu zai gana da shugabanni na kamfanonin da ke samar da lantarki a ƙasar domin tattaunawa kan bashin naira tiriliyan huɗu da suke bi.
Wata sanarwa da mai magana da yawun Ministan Lantarki Adebayo Adelabu ya fitar ranar Lahadi ta ce gwamnatin tarayya “ta ƙagu ta shawo kan matsalar” bayan ganawar da ministan ya yi da shugaban kamfanonin ranar Talata.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Yayin ganawar, ministan ya tabbatar wa kamfanonin da ake kira Generation Companies (GenCos) cewa gwamnati za ta mayar da hankali wajen wani ɓangare na bashin, in ji sanarwar.
“Akwai buƙatar mu biya wani babban ɓangare na kuɗin kuɗi hannu, idan ya so daga baya sai mu nemi a yi mana lamuni na biyan ragowar nan gaba,” a cewar ministan kamar yadda Bolaji Tunji ya ruwaito cikin sanarwar.
Ta ƙara da cewa za a daddale abin da gwamnatin za ta biya ne yayin ganawar tsakanin shugaban ƙasa da shugabannin kamfanonin.











