Shugaban Najeriya da majalisar ministoci ta ƙasar sun amince da sabon tsarin saye da kuma amfani da kayan da aka samar a cikin gida a dukkan ma’aikatun gwamnati.
Ministan Yaɗa Labarai Mohammed Idris ya faɗa wa manema labarai ranar Litinin cewa nan gaba kaɗan shugaban ƙasa zai sanya hannu kan wani umarni domin goyon bayan tsarin.
Read Also:
“Tsarin na nufin Najeriya za a fara sakawa a gaba a dukkan kayayyakin da za a sayo, babu wasu kaya ko na’urori da ake yi a cikin gida da za a sayo daga ƙasar waje ba tare da dalili ba,” in ji ministan bayan kammala taron majalisar. .
“Hakan zai sa gwamnati ta mayar da hankali kan jama’armu da masana’antunmu ta hanyar sauya yadda gwamnati ke mkashe kuɗi, da yadda muke sayo kaya, da ma yadda muke haɓaka tattalin arzikinmu.”
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1485 days 13 hours 36 minutes 33 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1467 days 15 hours 17 minutes 58 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com