Home General Gwamnatin Tinubu ta firgita da yunƙurin haɗaka – Atiku

Gwamnatin Tinubu ta firgita da yunƙurin haɗaka – Atiku

Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa gwamnatin Tinubu ta firgita da yunƙurin haɗakar jam’iyyun adawa inda ya ce har yanzu shi ne mafi ƙarfin ɗan adawa a Najeriya.

Ya bayyana hakan ne a matsayin martani ga kalaman Daniel Bwala, tsohon hadiminsa, wanda yanzu haka shi ne mai ba Shugaba Bola Ahmed Tinubu shawara kan harkokin sadarwar manufofi, inda ya shawarci Atiku da ya fasa ƙudirin sake tsayawa takara a 2027.

A wata hira da aka yi da shi a gidan talabiji na Channels, Bwala ya ce Atiku ya kamata ya yarda da ƙaddara, yana mai cewa wataƙila ba nufin Allah bane ya shugabanci Najeriya.

Ya kuma yi ikirarin cewa “Atiku ya rasa kashi 60 zuwa 70 cikin 100 na magoya bayansa, yana mai gargaɗin cewa ci gaba da wannan yunkuri na iya kai shi ga ƙarshe mai raɗaɗi.”

A martanin da ya fito daga ofishin yada labaran Atiku, an siffanta kalaman Bwala da “raini da kuma rashin mutunci,”.

Sanarwar ta ƙara da cewa “ceto da gina Najeriya aikin ne mai matuƙar muhimmanci na ƙasa — wanda bai kamata a bar shi yana tangal-tangal ba saboda son zuciyar wasu hadiman fadar shugaban ƙasa masu neman faranta ran kansu”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp