Home General Mutum 27 sun mutu a hatsarin kwale-kwale a Kwara

Mutum 27 sun mutu a hatsarin kwale-kwale a Kwara

Mutum 27 ne suka rasu bayan da kwale-kwalensu ya kife a karamar hukumar Kaiama na jihar Kwara.

Rahotanni sun bayyana cewa fasinjojin na kan hanyar su ne ta komawa gida daga kasuwa a jihar Neja, lokacin da jirginsu ya nitse.

Wani da ya tsira daga hatsarin, ya ce lamarin ya faru ne sakamakon ɗaukar kaya fiye da kima, kamar yadda gidan talabijin na Channels a Najeriya ya ruwaito.

Ya ce iska mai ƙarfi da ta taso musu – ita ma ta taimaka wajen kifar da kwale-kwalen, duk da cewa bai bayyana adadin mutanen da ke cikin jirgin ba.

Shugaban karamar hukumar ta Kaiama, Abdullahi Danladi, wanda ya jagoranci tawagar gwamnatin jihar don zuwa ta’aziyya ga iyalan waɗanda lamarin ya shafa, ya ce gwamnati ba za ta ci gaba da lamuntar samun hatsuran kwale-kwale da ake yi ba a kowace shekara.

Ya sanar da shirin kafa wani kwamitin da zai ɗabbaka saka rigunan kariya da hana tafiye-tafiye cikin dare da kuma aiwatar da sauran matakai na tsaro.

Hatsarin jirgin ruwan na zuwa ne watanni bakwai bayan samun irinsa da ya lakume rayukan mutane 100 a yankin.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp