Home Labarai Tinubu ya magantu kan wanda zai masa mataimaki a 2027

Tinubu ya magantu kan wanda zai masa mataimaki a 2027

Fadar Shugaban Kasa ta ce shugaba Bola Tinubu zai zabi wanda zai yi masa takarar mataimaki a zaben 2027 a hukumance ne kawai bayan a kammala babban taron jam’iyyar APC a 2026.

Kakakin shugaban, Bayo Onanuga ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawarsa da jaridar Daily Trust a ranar Alhamis.

Da yake martani kan dalilin da ya sa fadar shugaban ta yi shiru kan zargin cewa Tinubu na son canza mataimaki a 2027 musamman la’akari da yadda ’yan jam’iyyar ke ta nuna goyon bayansu ga shugaban shi kadai, Onanuga ya ce hakan ba gaskiya ba ne.

A cewarsa, “Lokacin da na karanta labarin, na karyata shi saboda ba shi da tushe. A tsarin shugaba mai cikakken iko da Najeriya ke bi, dan takarar shugaban kasa ake fara zaba, shi kuma sai ya zabi wanda zai yi masa mataimaki. Abin da ya faru ke nan a lokacin Buhari – an fara zabensa, sai daga baya shi kuma ya dauki mataimaki. Ba a yin duka biyun a lokaci daya.

“Da zarar INEC ta fitar da jadawalin zabuka, jam’iyya za ta shirya babban taronta, idan aka sake tsayar da shugaban kasa, shi kuma zai zabi mataimakinsa,” in ji Onanuga.

Kazalika, ya kuma yi fatali da tarihin da ake daukowa cewa sau biyu tinubu yana canza mataimaka lokacin da ya yi Gwamna a jihar Legas daga 1999 zuwa 2007, cewa irin haka za ta faru da Kashim Shettima a 2027.

Ya kuma ce jita-jitar da ake yadawa a kan yiwuwar canza Shettima tun ma kafin a fara nuna amincewa da sake takarar Tinubu ba ta da tushe.

Ya ce, “Ba ni da masaniya a kan duk wani sabani tsakanin shugaban kasa da mataimakinsa. Iya abin da na sani shi ne akwai kyakkyawar fahimtar juna da alakar aiki mai kyau a tsakaninsu.

Duk maganganun da ake yadawa ba su da maraba da na teburin mai shayi. Mutane na ta fadar maganganun marsa kan gado cewa wai Seyi Tinubu ne ma mataimakin shugaban kasa. Wannan shashanci ne.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp