Rundunar sojojin Najeriya ta samu gagarumar nasarar kashe manyan manyan kwamandojin Boko Haram da na tsagin ISWAP, a wasu hare-hare da ta kai a makon da ya gabata da kuma wannan makon da mu ke ciki.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
A wasu hare-hare da sojojin da ke aiki a ƙarƙashin rundunar Operation Hadin Kai suka kai garuruwan Mallam Fatori da kuma Buratai na jihar Borno a makon da ya gabata, sun samu nasarar kashe kwamandojin Boko Haram uku da suka haɗa da Amir Abu Ali da Amir Ibunu sai kuma Amir Abu Waldume.
Haka nan a wani harin na daban da suka kai Nzalgana na jihar Yobe da kuma Timbuktu na jihar Borno, jami’an tsaron na Najeriya sun kashe Ameer Malam Jidda, ɗaya daga cikin manyan kwamandojin Boko Haram a garin Ngorgore da Malumti.
Kisan manyan jagororin Boko Haram da sojojin Najeriya suka dai ya raunata tsarin shugabancinsu da kuma sanyasu cikin ɗimuwa.











