Home General Za mu ɗauki matakin hana sake faruwar kisan mutane – Gwamnatin Filato

Za mu ɗauki matakin hana sake faruwar kisan mutane – Gwamnatin Filato

Gwamnatin jihar Filato ta jaddada aniyarta ta ɗaukar mataki don hana sake faruwar kisan mutane a jihar bayan kisan wasu ƴan asalin jihar Kaduna a ƙaramar hukumar Mangu da ke jihar.

A makon jiya ne dai aka kashe wasu matafiya 12 ƴan Zaria, da ba su ji ba su gani ba, wani abu da ya janyo Allah-wadai daga ɓangarori daban-daban.

Joyce Ramnav, ita ce kwamishiniyar watsa labarai a jihar ta Filato, ta bayyanawa BBC cewa burinsu shi ne su nuna wa duniya cewa Filato jiha ce mai son zaman lafiya, mai maraba da mutane.

Ta ce, “jami’an tsaron sun kama mutum 22, kuma idan allah ya yarda gwamnati za ta ɗauki matakin domin a tabbatar an hukunta waɗannan mutane.”

Ta ce yanzu gwamnati na jiran sakamakon bincike ne da ƴansandan jihar ke gabatarwa, “kafin mu san matakin da za mu ɗauka na gaba.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
COAS Ya Bukaci Bojojin Nijeriya da su Mayar da Hankali Wajen Kare Rayukan Fararen HulaTURA TA KAI BANGO: Bayan Mutuwar Bashar Sani, Dole ne Arewa Ta Fuskanci MatsalolintaDangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige Fubara
X whatsapp