Home General Gwamnatin jihar Kano ta yi Alla-wadai da kisan ‘yan asalin jihar a...

Gwamnatin jihar Kano ta yi Alla-wadai da kisan ‘yan asalin jihar a Benuwai

Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba kabir Yusuf ya yi Alla-wadai da kisan matasa ‘yan asalin jihar a garin makurdi dake jihar Benuwai.
Wannan na cikin wata takardar sanarwa da Mai Magana da yawan Gwamnan kano Alhaji Abba Kabir Yusuf, Sanusi Bature Dawakin Tofa  ya fitar aka raba manema labarai a jihar Kano.
Sanarwar ta ce lamarin ya auku ga Matasan ne da misalin karfe 11: na daren litinin wanda kawo yanzu ba a kai ga gano wadanda suka aikata wannan aika-aikar ba.
Cikin bakin cikin gwamnan Alhaji Abba Kabir Yusuf ya bayyana kisan na rashin imani matsayin rashin hankali, wanda kuma ba za a lamunta ba.
Tun da fari dai an ruwaito matasan biyu da suka haɗar da Barham Sulaiman da Jamilu Ahmad ƴan asalin unguwa uku ne a jihar Kano.
Daga bisani sanarwa ta ce Gwamnan zai jagorancin wata tawagar ciki har da iyayen matasan domin gudanar da Jana’izarsu a babban masallacin ƙasa dake birnin Abuja.
 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp