Rundunar Sojin Najeriya ta tabbatar da mutuwar wasu daga cikin jami’anta sakamakon hare-haren da wasu ƴan bindiga suka kai kan sansanonin soji da ke jahohin Neja da Kaduna.
Rundunar ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafin sada zumunta na X.
A cewar sanarwar, hare-haren sun faru ne a ranar Litinin, 24 ga Yuni, 2025, a sansanonin sojin da ke Kwanar Dutse Mairiga da Boka a Jihar Neja, da kuma Aungwan Turai da ke ƙaramar hukumar Chikun a Jihar Kaduna.
Rahotanni sun ce ƴan bindigar sun kai hari ta ɓangarori uku a lokaci guda, lamarin da ya sa dakarun soji suka mayar da martani cikin gaggawa.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
A yayin musayar wuta ne rundunar soji ta tura dakarun ƙasa da na sama don fatattakar maharan, kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Rundunar ta ce an kashe ƴan bindiga da dama yayin gumurzun da ya ɗauki sa’o’i.
“Sai dai kuma, an kashe mana wasu jami’ai yayin musayar wuta da ƴan bindigar.”, in ji sanarwar.
Baya ga haka, rundunar ta kuma ce wasu sojoji huɗu sun jikkata sakamakon harbin bindiga kuma suna samun kulawar a asibiti.
Rundunar sojin ta bayyana waɗanda suka mutu a matsayin “jarumai” da suka tsaya tsayin daka wajen kare matsayinsu da mutuncin ƙasa.











