Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta a Najeriya INEC, ta tsaida ranar 16 ga watan Agustan wannan shekarar, don gudanar da zaɓukan cike gurbin ƴan majalisu a jihohi 12 na ƙasar.
Shugaban hukumar ta INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana hakan, yayin wata ganawa da shugabannin jam’iyyu da ya yi a Abuja a jiya Alhamis.
Ya ce an samu giɓin kujerun ne, sakamakon mutuwa da kuma hukuncin kotu da ya soke sakamakon wasu zaɓuka.
Read Also:
Za a gudanar da zaɓen ne a mazaɓu 16 da suka haɗa da sanatoci biyu da ƴan majalisar tarayya 5 sai kuma ƴan majalisar dokoki 9.
Shugaban na INEC ya ce hukumar za ta tura da jami’anta dubu 30 da ɗari 451 don gudanar da zaɓukan da mutane miliyan 3 da dubu dari 553 da ɗari 659 za su kaɗa kuri’a a rumfunar zaɓe dubu 6 da ɗari 987.
Sai dai ya ce ba za su gudanar da zaɓe a mazaɓar Khana ll da ke jihar Rivers bisa dokar taɓaci da aka sanya, da kuma mazaɓar Talata Mafara ta Kudu da ke jihar Zamfara, sakamakon rashin kammala shari’ar da ake yi a kai.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1471 days 8 hours 39 minutes 9 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1453 days 10 hours 20 minutes 34 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com