Home General Tinubu zai saka hannu a sabuwar dokar haraji da ta yamutsa hazo

Tinubu zai saka hannu a sabuwar dokar haraji da ta yamutsa hazo

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu zai sanya hannu kan sabbin dokokin sauya tsarin haraji na ƙasar a yau Alhamis, a wani mataki da ake sa ran zai sauya tsarin tattara haraji da kuma inganta yanayin kasuwanci a Najeriya.

Sanarwar da fadar shugaban ƙasar ta fitar ta hannun mai taimaka masa kan yaɗa labaru, Bayo Onanuga ta ce sabbin dokokin huɗu sun haɗa da dokar haraji ta ƙasa da dokar tafiyar da lammuran haraji da dokar kafa hukumar haraji ta Najeriya da kuma dokar kafa ma’aikatar kula da hukumomin tattara haraji ta Najeriya.

Majalisar Dokoki ta kasa ce za ta amince da su bayan shawarwari da dama daga masu ruwa da tsaki.

Sabbin dokokin harajin na Najeriya sun tayar da ƙura sosai a lokacin da shugaban ƙasar ya gabatar da su ga majalisar dokokin ƙasar, lamarin da ya kai ga dakatar da tattaunawa a kan su a zauren majalisar.

Tun da farko gwamnonin jihohin ƙasar da majalisar kula da tattalin arziƙi ta Najeriya da ƙungiyoyi sun buƙaci a sake duba dokar kafin sake gabatar da ita.

Daga baya gwamnonin jihohin ƙasar sun gudanar da gyare-gyare kan dokar tare da gabatar wa shugaban ƙasa, wanda ya amince da su kafin majalisar dokokin ƙasar ta ci gaba da muhawara.

Majalisar dokokin ƙasar ta ce a halin yanzu an gyara duk wasu ɓangarori da suka haifar da tayar da jijiyoyin wuya.

Sai dai har yanzu al’umma da dama ba su da cikakkiyar masaniyar abubuwan da dokokin suka ƙunsa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
HOTO: NSCDC ta Tsare Jami'ai 24 Kan Mutuwar Masu Hakar Ma'adinai a TsareShirin Tallafin Mai: Atiku ya yi Watsi da Gaskiyar Magana – APCGwamnatin Tarayya ta Inganta Samar da Abinci ta Hanyar Shirin AgriShield na ONSA Daga Chido OnumahAtiku ya yi Tambaya Kan Rashin Zuwa UNGA a Karo na Uku da Tinubu ya yi, ya Nemi Karin BayaniFalconets ta Fice Daga Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata Ƴan Kasa da Shekaru 20 Bayan Colombia ta Sha Kashi a Wasan KarsheMatawalle Ya Nemi Tallafin Czech Don Samar da Alburusan DICON da Canja FasahaRundunar Sojojin Najeriya Ta Tallafa wa Iyalan Sojojin Gambia da Suka MutuFilato: Sojoji Sun Kama Masu Garkuwa 11, Sun Kwato MakamaiOPHK ta yi Bayani Kan Rahoton Amnesty na 2016 Dangane da Mutuwar da Ake Zargi a Barkin Giwa2027: Sama da Mambobin Jam'iyyar NDC 6,000 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a EnuguKwankwaso ya Nuna Aniyar Yin Sulhu da Gwamna YusufYadda Hon. Hudu Kanje Ya Sake Fasalin Jagorancin Cigaban Kasa Daga Mika'il Ja'afarƳan Sanda Sun Kama Mutane 300 a Farmakin Wuraren da Ake Aikata Laifuka a FCT Sun Kwace Wukake, Bindigar Wasa, da WiwiZakari Mohammed: Dole Kwara ta Cika Kwarewarta – Dan Takarar ADC ya Nemi Muhawara a BayyaneWSCIJ ta Yaba wa PRNigeria Kan Ci Gaba da Tallafawa Matasa Wajen Sadarwa Bayan Karewar Tallafi
X whatsapp