Home General Sojojin Najeriya sun kai farmakin ramuwar gayya kan ƴan bindiga a Neja

Sojojin Najeriya sun kai farmakin ramuwar gayya kan ƴan bindiga a Neja

Dakarun Sojin Saman Najeriya sun ce sun ƙaddamar da gagarumin farmakin sama kan sansanonin ‘yan bindiga a jihar Neja a ranakun Laraba da Alhamis, a wani yunƙuri na kawar da ƴan fashin da suka kai hari kan dakarun ƙasar a baya-bayan nan.

Wata sanarwa da rundunar sojin saman ta wallafa a shafinta na sada zumunta ta ce an kai harin ne ƙarƙashin shirin FANSAN YAMMA “domin kawar da barazanar tsaro da ‘yan ta’adda ke haifarwa.

“A ranar 26 ga watan Yuni, bayan samun bayanan sirri, rundunar sojin saman Najeriya, bayan haɗa gwiwa da sauran jami’an tsaro ta gano ayyukan ƴan bindiga da suka hada da satar shanu a yankin Kakihun da Kumbashi,” in ji sanarwar wadda ta samu sa hannu daraktan yaɗa labarai na rundunar Air Commodore Ehimen Ejodame.

“Nan take rundunar ta ƙaddamar da hare-haren da suka yi sanadin kashe ƴan fashin daji da dama, lalata kayan aikinsu da kuma hana su haɗuwa,” kamar yadda sanarwar ta bayyana.

A cikin makon nan ne aka samu rahotannin da suka ce ƴan fashin daji a jihar ta Neja, arewa maso tsakiyar Najeriya sun kai samame a wasu sansanonin sojin Najeriya inda suka kashe jami’an soji “aƙalla 17”.

Wata sanarwa da rundunar sojin ƙasa ta Najeriyar ta fitar ta tabbatar da kai harin sai dai ba ta yi bayani kan yawan sojojin da suka rasa rayukansu ba sanadiyyar farmakin.

Neja na cikin jihohin Najeriya masu fama da matsalar tsaro, inda ƴan bindiga suka tarwatsa ƙauyuka da dama, lamarin da ya haifar da asarar ɗimbin rayuka da kawo cikas ga ayyukan tattalin arziƙi

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Gwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanciGwamnatin Najeriya da gwamnonin APC sun bai wa ƴan kasuwar Singer tallafin biliyan 8Kwankwasiyya ta yi martani kan matakin majalisar Amurka na hukunta KwankwasoSojojin Najeriya sun daƙile hare-haren mayaƙan ISWAP a BornoFarfesa Abdullahi Pakistan ya bayyana dalilinsa na ajiye shugaban Hukumar NAHCONMajalisar Najeriya ta kafa kwamitin nazari kan gyaran dokar zaɓeRundunar sojin Najeriya ta tura dakaru na musamman zuwa Filato don daƙile ƴanbindigaMajalisar Dinkin Duniya da Turkiya sun yi Alla-wadai da harin da aka kai KwaraAmurka ka iya sake kai Hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci- TrumpAmurka ka iya sake kai hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci
X whatsapp