Home General Shugaba Tinubu ya mika ta’aziyyar Alhaji Aminu Dantata

Shugaba Tinubu ya mika ta’aziyyar Alhaji Aminu Dantata

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya aike da saƙon ta’aziyarsa ta rasuwar Alhaji Aminu Ɗantata, attajirin ɗankasuwa da ya rasu a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, wanda ya rasu yana da shekara 94 a duniya.

Tinubu ya bayyana rasuwar hamshaƙin ɗankasuwar, wanda aka binne a ƙasar Saudiyya a matsayin “rashi ga ƙasar baki ɗaya’.

Tinubu ya yaba da gudunmuwar da marigayin ya bayar wajen ciyar da Najeriya gaba, “musamman a ɓangaren ilimi da kiwon lafiya,” kamar yadda sanarwar da mai magana da yawun shugaban, Bayo Onanuga ya fitar.

Tinubu ya ce, “mun yi rashi na babban ɗankasuwa, mai kishin ƙasa, kuma dattijon arziki wanda ya ya taimaka wajen gina ƙasarmu Najeriya.”

Tinubu ya ce za a riƙa tuna Ɗantata a matsayin ɗankasuwa mai sanin ya kamata wanda ya bayar da gudunmuwa wajen haɗin kan ƙasa ta hanyar kasuwancinsa da ayyukan jinƙai, “wanda amfanar da ƴan Najeriya da ba za su ƙirbu ba.”

A ƙarshe Tinubu ya jajanta wa iyalan marigayin tare gwamnati da al’ummar Kano baki ɗaya bisa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp