Ikirari: Ta cikin wani bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta kamar Facebook, TikTok, da Instagram, ya nuna wani mutum da ake cewa ya kama matarsa da direbansa suna aikata zina a wani ɗakin otal.
Bidiyon ya nuna wasu mutane biyu daya na bin daya a baya kamar yana masa jagora don nuna masa wani muhimmin abun da ya shafe shi kai tsaye. Aka rufo bayan bidiyon da wani sako dake cewa: “WA ZA A YI AMINCEWA A YANZU..??? INNALLILLAHI-WA-INNA-ILLAIHI-RAJIUN – DON ALLAH YANA DA MUHIMMANCI KA KALLA..!!!”
Ra’ayoyin da suka biyo baya sun nuna mamaki da tashin hankali, inda mutane da dama suka nuna jin takaici. Wani sharhi da ya yadu sosai ya ce: “Ba kawai yana tukin motarsa ba, har da matarsa ma yana ‘tukawa’?”
Mafi yawan lokaci Musulmi kan yi amfani da Kalmar “Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un” idan masifa ta samesu kamar yadda addinin musulunci ya yi umarni a cikin Al’kurani mai tsarki, an yi amfani da Kalmar ana domin nuna girman abin da ya faru.
Bidiyon ya haddasa fushi da tausayawa a kafafen sada zumunta. Wasu sun zargi matar da direban, yayin da wasu suka nuna shakku game da sahihancin lamarin.
Read Also:
BINCIKE SHAHIHANCIN LABARI: Domin tantance sahihancin bidiyon, Tawagar PRNigeria ta gudanar da binciken fasaha da amfani da kayan aikin binciken hoto da nazarin ko wane bangare ba bidiyon.
Ga abin da muka gano:
Bidiyon ya fara bayyana sosai a shafukan sada zumunta a makon farko na Yuli 2025.
Mutumin da ya jagoranci mijin cikin ɗakin otal ɗin, an gano cewa sanannen mai ƙirƙirar bidiyoyi ne a kafafen sada zumunta, yana da sama da mabiya 10,000 a Instagram da mabiya sama da miliyan 1 a dandalin Facebook.
Binciken PRNigeria ya tabbatar da cewa bidiyon wani ɗan wasan barkwanci ne mai suna Mumin Nuhu, wanda ke amfani da sunan “The Honour”.
Bidiyon gaba ɗaya shirin film ne da aka tsara don nishadantarwa, Asalin bidiyon da aka wallafa a Facebook ya samu kusan ra’ayoyi miliyan ɗaya, mutane 8,200 sun yada shi yayin da 3,300 suka tofa albarkacin bakinsu akai.
“The Honour” na daga cikin wadanda ke ƙirƙirar bidiyoyin da suka shafi soyayya, yaudara, da cin amana. Yana amfani da irin wannan salo da tsarin labari a yawancin sauran bidiyoyinsa.
KAMMALAWA: PRNigeria ta tabbatar cewa wannan bidiyo da ke yawo a matsayin matar aure da direbanta suna zina, ba gaskiya ba ne. wasan kwaikwayo ne da aka yi don jan hankalin mutane a kafafen sada zumunta.
HUKUNCI: Bidiyon labarin bai faru a gaske ba, wasan kwaikwayo ne da aka tsara ta hannun wani sanannen mai bidiyon barkwanci.
Daga PRNigeria
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1495 days 9 hours 40 minutes 52 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1477 days 11 hours 22 minutes 17 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com