Gwamnatin Filato ta zargi jami’an tsaro da rashin kama maharan jihar

Gwamnatin jihar Filato da ke tsakiyar Najeriya ta zargi jami’an sojojin ƙasar da sakaci wajen rashin kama maharan da suka kashe mutum 27 a garin Tahoss na yankin ƙaramar hukumar Riyom.

A farkon makon nan ne wasu mahara ɗauke da makamai suka auka wa garin tare da halaka mutum 27 da raunata wasu.

Yayin wata hira da gidan talbijin na Channels ranar Juma’a ta cikin shirin ”The Morning Brief” kwamishiniyar yaɗa labaran jihar, Joyce Ramnap ta ce sojojin da ke yankin sun nuna sakaci wajen rashin kama ko da mutum guda cikin maharan, duk kuwa da kasancewar sojojin a kusa da garin.

Kwamishiniyar ta ce garin da aka kai harin na kusa da shingen binciken ababen hawa da sojoji ke gudanarwa.

“Akwai shingen binciken ababen hawa na sojoji, wanda bai fi tazarar mita 200 daga wurin da lamarin ya faru, kuma daga bayanan da muka samu ba wanda suka kama, kuma ba su kashe kowa ba”.

“Garin nan ba wani gari ba ne mai nisa da za a ce kafin a kai inda suke an yi musu lahani, suna kusa da titi,” in ji ta.

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1492 days 2 hours 33 minutes 1 second,

Baptist School Students, Kaduna
1474 days 4 hours 14 minutes 26 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com