Babbar Kotun Tarayya mai lamba 3 da ke Kano ƙarƙashin jagorancin Mai shari’a Simon Amobeda ta kori karar da jam’iyyar APC da Hon. Abdullahi Abbas da Hon. Aminu Aliyu Tiga suka shigar domin hana biyan kuɗaɗen kananan hukumomi a Kano.
Read Also:
Masu ƙarar sun nemi hakan ne bisa hujjar cewa an saba umarnin kotu da ya hana gudanar da zaɓen.
A zaman kotun lauyan masu ƙara ya nemi a jingine shari’ar, amma lauyan gwamnatin Kano ya nemi a kori ta tare da biyan diyya.
A karshe Kotun dai ta yanke hukunci da korar karar baki ɗaya.