Home General Za a yi ruwan sama da iska mai ƙarfi a sassan Najeriya...

Za a yi ruwan sama da iska mai ƙarfi a sassan Najeriya – NiMET

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya (NiMET) ta fitar da hasashen yanayi na kwana uku, daga Litinin 21 zuwa Laraba 23 ga Yulin 2025, inda ta bayyana cewa za a samu ruwan sama da iska mai ƙarfi a sassa daban-daban na ƙasar.

A kan haka NiMet ta shawarci al’umma da su yi taka-tsantsan kan yiwuwar samun ambaliya da kuma ɓarna da iska mai ƙarfi ke iya haddasawa.

A cewar sanarwar da hukumar ta wallafa a shafin sada zumunta na X, jihohin Arewa da na Kudu da kuma yankin tsakiya, duk za su fuskanci iska mai ƙarfi haɗe da ruwan sama.

Hasashen ya nuna cewa a ranar Litinin da safe, an samu ruwan sama da iska a jihohin Taraba da Adamawa da Kebbi da Borno da Yobe da Gombe da Bauchi da Sokoto da Kaduna.

Ya kuma nuna cewa yankin tsakiyar kasar kamar Abuja da Niger da Plateau da Nasarawa da Benue da Kogi su ma za su samu ruwan sama daga rana zuwa yamma.

Ranar Talata da safe kuma ana sa ran ruwan sama da tsakar rana a Abuja da Kwara da Niger da Plateau.

A ranar Laraba da safe kuma, za a samu iska mai ƙarfi da ruwa a Katsina da Kano da Bauchi da Sokoto da Taraba sannan daga baya za a samu a Yobe da Jigawa da Kaduna da Borno da kuma Kebbi.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Gwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanciGwamnatin Najeriya da gwamnonin APC sun bai wa ƴan kasuwar Singer tallafin biliyan 8Kwankwasiyya ta yi martani kan matakin majalisar Amurka na hukunta KwankwasoSojojin Najeriya sun daƙile hare-haren mayaƙan ISWAP a BornoFarfesa Abdullahi Pakistan ya bayyana dalilinsa na ajiye shugaban Hukumar NAHCONMajalisar Najeriya ta kafa kwamitin nazari kan gyaran dokar zaɓeRundunar sojin Najeriya ta tura dakaru na musamman zuwa Filato don daƙile ƴanbindigaMajalisar Dinkin Duniya da Turkiya sun yi Alla-wadai da harin da aka kai KwaraAmurka ka iya sake kai Hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci- TrumpAmurka ka iya sake kai hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci
X whatsapp