Home Labarai Majalisar dattawa ta amince da buƙatar Tinubu na ciyo bashin dala biliyan...

Majalisar dattawa ta amince da buƙatar Tinubu na ciyo bashin dala biliyan 21

A ranar Talata ne majalisar Dattawa ta amince da buƙatar Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta ciyo bashin kuɗi daga ƙasashen waje da ya kai sama da dala biliyan 21 domin kashewa tsakanin shekarar 2025 zuwa 2026

Amincewar ta biyo bayan gabatar da rahoton kwamitin majalisar dattawa kan bashi daga cikin gida da waje, wanda shugaban kwamitin, Sanata Aliyu Wamakko, ya gabatar.

Akwai kuma shirin tara dala biliyan 2 daga cikin gida.

Tinubu ya ce za ayi amfani da bashin kuɗaɗen ne kan ɓangarorin gine-gine da noma da tsaro da wutar lantarki da fasahar sadarwa.

An ware dala biliyan 3 don farfaɗo da layin dogo daga Fatakwal zuwa Maiduguri.

Sanatoci da dama sun goyi bayan wannan shirin, inda suka ce hakan yana nuna adalci ga kowane yanki na ƙasar, kuma yana cikin tsarin da duniya ke bi wajen ci gaban tattalin arziki.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp