Home Labarai Dino Melaye ya koma jam’iyyar ADC bayan ficewarsa daga PDP

Dino Melaye ya koma jam’iyyar ADC bayan ficewarsa daga PDP

Tsohon ɗan jamalisar dattawan Najeriya mai wakiltar Kogi ta Yamma ya koma jam’iyyar haɗakar ADC bayan ficewarsa daga PDP.

Cikin wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na X, an ga yadda Dino Melaye ya karɓi katin jam’iyyar ADC daga hannun jagororin jam’iyyar na ƙaramar hukumarsa.

Tun da farko a yau ne Dino Melaye ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar PDP bayan ya rubuta wa jagororin jam’iyyar na mazaɓarsa ta Aiyetoro Gbede wasiƙar ficewarsa daga jam’iyyar.

A cikin wasiƙar Melaye ya bayyana dalilan kasawar jam’iyyar wajen magance matsalolin da ke damunta.

”Matakin ya zama wajibi saboda gazawar jam’iyyar wajen ceto yan Najeriya daga cikin kuncin da ƙasarmu ke ciki”, kamar yadda wasiƙar ta bayyana.

Tsohon ɗan takarar gwamnan jihar Kogin na jam’iyyar PDP ya ce ya ɗauki matakin ne bayan dogon nazari kan halin da jam’iyyar ke ciki.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Gwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanciGwamnatin Najeriya da gwamnonin APC sun bai wa ƴan kasuwar Singer tallafin biliyan 8Kwankwasiyya ta yi martani kan matakin majalisar Amurka na hukunta KwankwasoSojojin Najeriya sun daƙile hare-haren mayaƙan ISWAP a BornoFarfesa Abdullahi Pakistan ya bayyana dalilinsa na ajiye shugaban Hukumar NAHCONMajalisar Najeriya ta kafa kwamitin nazari kan gyaran dokar zaɓeRundunar sojin Najeriya ta tura dakaru na musamman zuwa Filato don daƙile ƴanbindigaMajalisar Dinkin Duniya da Turkiya sun yi Alla-wadai da harin da aka kai KwaraAmurka ka iya sake kai Hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci- TrumpAmurka ka iya sake kai hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci
X whatsapp