Shugabn Nijeriya Bola Tinubu ya karawa shugaban hukumar hana fasa kwauri ta kasa (Custom) Bashir Adewale Adeniyi wa’adin aiki na shekara guda.
Wannan dai na zuwa ne daidai lokacin da wa’adin aikin nasa zai kare karshen wata mai kamawa wato 31 ga watan Agustan 2025.
Ta cikin wata sanarwa daga Fadar Shugaban Ƙasa da Bayo Onanuga, Mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan Harkokin Bayani da Tsare-tsare, ya sanya wa hannu, wadda ta ce ƙarin wa’adin na da nufin bai wa Adeniyi damar kammala sauye-sauyen da ake aiwatarwa tare da cika manyan manufofin gwamnatin Bola Tinubu.
Read Also:
Ayyukan da ake son kammalawa sun haɗa da sabunta tsarin aikin Hukumar Kwastam, aiwatar da tsarin National Single Window Project, da kuma cika alƙawarin da Najeriya ta ɗauka a ƙarƙashin yarjejeniyar ciniki ta nahiyar Afirka (AfCFTA).
Shugaba Tinubu ya yabawa Adeniyi bisa “ƙwazo da ya nuna wajen jagoranci da da kuma hidimatawa,” yana mai bayyana tabbacin cewa ƙarin wa’adin zai ƙarfafa rawar da Hukumar Kwastam ke takawa a fannin sauƙaƙe cinikayya, haɓaka kuɗaɗen shiga, da kuma tsaro a kan iyakoki Nijeriya.
PRNigeria