Ma’aikatar harkokin tsaron Amurkar ta ce gwamnatin kasar ta amince ta sayar wa Nijeriya makamai da kuɗinsu ya kai dala miliyan 346
gwamantin kasar ta ce makaman da za a sayar wa Najeriyar sun haɗa da manyan bama-bamai da kuma rokoki, wanda sayar da makaman zai ƙara inganta ɓangaren tsaron Najeriya da kuma taimakawa tsarin harkokin wajen ta a yankin kudu da Hamadar Saharar Afirka.
“Cikin makaman har da wasu rokoki na zamani sama da 5,000,” in ji sanarwar Washington.
A 2014 lokacin mulkin Barack Obama, Amurka ta ki amincewa ta sayar wa Najeriya wasu muggan makamai, bayan nuna damuwa kan zargin sojojin ƙasar da take hakkin ɗan’adam.
A lokacin, gwamnatin Najeriya ta yi ƙorafin cewa hakan na yin cikas a yaƙi da take yi da masu tayar da kayar baya a arewa maso gabashin kasar.
Har zuwa yau, Nijeriya na ci gaba da fuskantar matsalolin tsaro da suka haɗa da hare-hare da ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadi ke kai wa da kuma ayyukan masu garkuwa da mutane a arewa maso yamma da kuma ƴan awaren Biafra a kudu maso gabashin ƙasar.