Gwamnonin PDP na taro a Zamfara

Gwamnonin jam’iyyar PDP a Najeriya na gudanar da wani taro a jihar Zamfara domin tattaunawa kan yunƙurinsu na “ɗaukar matakai masu muhimmanci”.

Taron zai fara ne daga yau Juma’a bayan hallarar gwamnonin, inda ake sa ran tattaunawa kan muhimman batutuwa a gobe Asabar.

A cikin sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ya bayyana cewa, taron na nufin tattauna muhimman batutuwan siyasa da gwamnonin ke fuskanta a halin yanzu.

PDP, wadda ita ce babbar jam’iyyar adawa a Najeriya na fuskantar ƙalubale na rikicin cikin gida da kuma ficewar wasu daga cikin manyan ƴaƴanta, ko dai zuwa jam’iyyar APC mai mulki ko kuma wadanda ke alaƙanta kansu da haɗakar ƴan adawa waɗanda suka tare a jam’iyyar ADC.

Hakan na faruwa ne gabanin babban zaɓen ƙasar na 2027. inda ƴan siyasa a kasar ke ci gaba da shiri, duk kuwa da gargadin da hukumar zaɓen ƙasar mai zaman kanta ta ƙasar ta yi kan fara harkokin siyasa gabanin lokaci.

A cikin sanarwar da gwamnan ya fitar ya ce “taron zai mayar da hankali kan batutuwan da suka shafi haɗin kan jam’iyyar da kuma shirin bunƙasa ci gaban jihohi, musamman a lokacin da jam’iyyar ke shirin gudanar da babban taronta na kasa a garin Ibadan, a ranakun 15 da 16 ga Nuwamba, 2025.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com