Gwamnatin Jihar Katsina, ta ce dakarun sojin Najeriya sun kashe ’yan fashi bakwai a jihar.
Read Also:
Ya kara da cewa samamen ya ɗauki sama da awa biyu a ranar Alhamis, bayan samun bayanan sirri cewa ’yan fashin sun kai hari ƙauyen Baba.
Wannan lamari ya faru ne kwanaki kaɗan bayan wani hari da ’yan fashi suka kai wani masallaci.
Harin ya yi sanadin salwantar rayukan sama da mutane 30, rahotanni kuma na cewa adadin ya kai kusan 50.