kungiyar Miyetti Allah ta ce akalla Fulani makiyaya 20,000 aka kashe a rikicin manoma da makiyaya, yayin da aka sace musu shannu sama da miliyan 4 a cikin shekaru 5 da suka gabata,
Shugaban ƙungiyar Fulani ta Miyetti Allah a Najeriya Baba Usman Ngelzerma ne ya bayyana hakan lokacin da yake kare kan su daga zargin cewar basa ɗaga muryarsu a duk lokacin da aka samu ɓatagari daga cikin su dake gudanar da ayyukan ta’addanci a Najeriya.
Ngelzerma ya ce su kan su Fulani makiyayan ba su tsira daga ayyukan waɗannan ɓatagari ba, domin ko a watannin da suka gabata, an hallaka shugabannin su na jihohin Katsina da Kwara da kuma Filato, saboda haɗa kan da suke yi da hukumomi domin dakile ayyukan ta’addanci a jihohin da suke shugabanci.
Shugaban ƙungiyar ya ce tabbas wannan matsala ta ayyukan ta’addanci ta ɓatawa Fulani suna a Najeriya, amma kuma ba dukkan su ke cikin wannan aiki ba, domin akwai Fulani na gari dake gudanar da ayyukan su cikin kwanciyar hankali, ba tare da goyan bayan ta’addancin ba.
Ngelzerma ya ce yanzu haka tsakanin Fulani makiyaya dubu 15,000 zuwa 20,000 suka fice daga Najeriya zuwa wasu ƙasashe domin tsira da rayukan su da kuma dukiyoyin su daga waɗannan ƴan ta’adda da suka hana gudanar da kiwo cikin kwanciyar hankali.
Read Also:
Shugaban ya ce ko a ƴan kwanakin da suka gabata, shanu sama da 10,000 aka kwacewa wasu makiyaya a jihar Kebbi, kana kuma aka kora su cikin gonakin manoma, da zummar haddasa rikici, domin nuna wa duniya cewar Fulani makiyaya ne suka sanya shannun a cikin gonaki, alhali kuwa ɓarayi ne suka kora su ciki.
Ngelzerma wanda ya bayyana cewar suna haɗa kai da gwamnoni da kuma jami’an tsaro wajen ganin an dakile ayyukan ta’addanci, ya bukaci a dinga yiwa Fulanin adalci, musamman ganin yadda su ma suke rasa rayukan su da kuma dukiyoyin su daga waɗannan ɓatagarin dake amsa sunan Fulani.
Shugaban ya yi misali da abinda ke faruwa a jihar Anambra, inda gwamnan jihar ya tabbatarwa duniya cewar ba Fulani ne ke gudanar da ayyukan ta’addanci a jiharsa ba, saɓanin yadda ake hasashe koda yaushe.
Gwamna Chukwuma Soludo ya shaidawa duniya lokacin da ya ziyarci Amurka cewar kashi 99 na ayyukan ta’addanci da ake samu a jiharsa, ƴan kabilar Igbo ne ke aikatawa.
Sai dai shugaban Fulanin ya ce yayin da gwamnonin kudu ke haɗa kai da su wajen samun maslaha dangane da irin waɗannan ayyukan ta’addanci, gwamnonin arewa basa ba su haɗin kan da ake buƙata wajen tainkarar matsalar, wadda ta zama ruwan dare gama duniya a jihiohi da dama, musamman yankin arewa maso yamma da kuma jihohin Benue da Filato.
Ngelzerma ya ce an sha samun waɗanda ba Fulani ba dake shigar burtu a wasu jihohi, musamman Filato wajen aikata laifi da zummar shafawa Fulanin kashin kaji, amma a ƙarshe sai jami’an tsaro su yi nasarar gano su.
Shugaban Miyetti Allahn ya ce za su ci gaba da haɗin kai da hukumomi domin ganin an shawo kan wannan matsalar da ta hana jama’a zaman lafiya a koda yaushe.