Rundunar ƴan sanda Jihar Jigawa ta samu nasarar cafke mutane 13 da ta ke zargi da dillancin miyagun ƙwayoyi a jihar dake arewa maso yammacin Nijeriya.
Wannan dai na cikin wata sanarwa da Kakakin rundunar SP Shiisu Lawan Adam, ya fitar wadda ta ce dakarun rundunar sun gudanar da wani sumame a sassan jihar daga ranar 2 zuwa 6 ga watan satumbar 2025, wanda aka shirya shi bayan samun wasu bayanan sirrin da hukumar ta yi kan masu safarar miyagun ƙwayoyi da wasu masu tayar da hankulan jama’ar jihar.
Read Also:
Sanarwa ta kara da cewa dakarun suna gudanar da sumamen ne a sassana jihar da suka hadar da Dutse, Guri, Birnin Kudu, Bamaina, Babura da Roni, kan maɓoyar masu laifin da wuraren da suke gudanar da safarar miyagun ƙwayoyin, inda aka kama mutane 13 waɗanda suka haɗa da Basiru Garba, Ladan Muhammad, Hassan Ali, Abubakar Sa’adu, Ahmad Muhammad, Aminu Hamisu, Muhammad Abdullahi, Suleiman Abdullahi, Abubakar Auwalu, Faruk Abdullahi, Isah Ismail, Hassan Aliyu, da Usman Muhammad – dukkaninsu daga sassa daban-daban na Jigawa da Nguru, Jihar Yobe.
A yayin samamen, jami’an ƴan sandan sun ƙwato miyagun ƙwayoyi iri-iri ciki har da Exol guda (704), Tramadol (264), Diazepam (3), D5 (2,042), roba mai wari (48), tabar wiwi (4 blocks da 148 wraps), wayar Vivo (da ake zargin ta sata ce), farare da jajayen kafso (602), da wasu kayan maye sanfurin ruwa har lita 6.
Sanarwar ta ce an miƙa waɗanda ake zargi zuwa kotu bayan kammala cikakken bincike.
Kwamishinan ƴan sandan Jihar Jigawa, CP Dahiru Muhammad, ya gargaɗi duk masu aikata miyagun laifuka da su daina ko kuma su fuskanci hukuncin doka, tare da kira ga jama’a da su ci gaba da bayar da bayanai masu inganci domin taimakawa rundunar wajen dakile aikata laifi.
Sanarwar ta ƙare da tabbatarwa jama’a cewa rundunar ƴan sanda na ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da zaman lafiya, tsaro da kwanciyar hankali a dukkan ƙananan hukumomin jihar.