Fadar shugaban ƙasa ta maida martani kan rahoton Bankin Duniya da ya ce mutane miliyan 139 na rayuwa cikin talauci a Najeriya, inda ta ce ƙididdigar ba ta nuna hakikanin halin da ake ciki a ƙasar ba.
A cewar fadar shugaban ƙasa, Bankin Duniya ya yi amfani da ƙa’idar duniya wadda ke ɗaukar duk wanda ba ya samun sama da dala $2.15 a rana a matsayin talaka.
Wannan ƙa’ida an kafa ta ne tun shekarar 2017, kuma idan aka fassara ta zuwa kuɗin Najeriya a yau, ta kai kusan Naira 100,000 a wata fiye da sabon mafi ƙarancin albashi na Naira 70,000 kenan.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Fadar shugaban ƙasa ta fitar wanda Sunday Dare, mai magana da yawun shugaban ƙasa ya fitar a shafinsa na X.
‘Bayanan da Bankin Duniya ya dogara da su tsofaffi ne tun daga shekarar 2018/2019, kuma ba su haɗa da tattalin arzikin yanzu ba. Saboda haka, gwamnati ta bayyana cewa wannan adadi misali ne na ƙididdigar duniya, ba ainihin yanayin da ake ciki a shekarar 2025 ba.”
A cewar fadar shugaban ƙasa, abin da ya fi muhimmanci shi ne hanyar da ake bi wajen farfaɗo da tattalin arzikin ƙasa, amma kuma Bankin Duniya ta ce sauye-sauyen Tinubu ba su rage talauci ba.
Ta ce “gwamnatin Shugaba Tinubu tana mai da hankali ne wajen rage wahalar tattalin arziki ta hanyar shirye-shirye na musamman kamar tallafin kuɗi ga talakawa, da bashin karatu na ɗalibai, da sauransu.”










